10 Agusta 2021 - 11:14
Iran: An Bukaci A Gudanar Da Makokin Imam Husain(a.s) Cikin Tsarin Kula Da Kiwon Lafiya

Ministan harkokin cikin gida na kasar Iran Abolreza Rahmani Fadli ya yi kira da masu makokin kwanaki 10 na watan muharram sun gudanar da makokin cin tsarin kiwon lafiya wanda kwamitin yaki da cutar Covid19 na kasa ya bayar.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Iran Press (IP) ya nakalto ministan yana fadar haka a jiya litinin ya kuma bukaci gwamnoni lardunan kasar su sanya ido a tarurrukan makakon da ake gudanarwa a larduninsau don tabbatar da an kiyaye wadandan tsare-tsare na kiwon lafiya don kare lafiyar Jama’a.

Yau talata ce daya ga watan muharram na na sabuwar shekara ta 1443 bayan hijirar manzon Allah (s) daga Makka zuwa Madina. Kuma daga yau mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah (s) suke zaman makokin shahadir Imam Husain(a) jikan manzon All..(s) wanda yayi shahada a hannun sarakunan bani Umayya a shekara ta 60 bayana hijira. Rayuwa wannan wadannan kwanaki na makoki sunnan ce mai karfi ga muminai.

342/